pacman, rainbows, and roller s
Google69490f6862051cb8
google-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlBasheer journalist sharfadi14

Basheer journalist sharfadi14.jpg6
Basheer journalist sharfadi 11 1
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka 1

☀ Zabi inda kake son shiga ☀
Menunks
→Home
→Akidojin Ahlussunnah
→Addinin musulunci (35)
→40 Hadith (50)
→Fadakarwa (120)
→Neman labarai (20)
→Shi'a Kafirci (50)
→Hadith (55)
→Khudubobi (24)
→Tarihin magabata (60)
→Raddi / Maida martani (99)
→Face book post (30)
→Monthly Archives (60)
→Tambaya da Amsa (20)
→Sahabban Annabi {s.aw} (50)
→Taskar maluman sunnah (25)
→Akidar Y'an Shi'a Dangane da Al'kur'ani
→Fassarar Usulussunnah (20)
→Sheik Ja'afar {Rahimahullah} (65)
→Sheik Abubakar Gumi {Rahimahullah} (30)
→Sheik Dr. Muhammad Sani R/Lemo
→Salafiyyah Network Nigeria (100)
→Adam Sani Abu-Umayrah (99)
→Salaf Ustaz (79)
→Malama Ummi Ahmad Katsina
→Malama Amina Saleh Mande
→Labarai (40)
→Nishadantarwa (10)
→Siyasar Nigeria (9)
→Vidio (33)
→Audio (66)
→Hotuna (120)
→Internet Cheat (90)
→Site Achieve
→Application (10)
→Games (8)
→About me (01)

Wannan shafin mallakarCoollogo com-1281358 3
Ne




SHAFI DON KARUWAR MUSULMI
**AKIDOJIN AHLUSSUNNAH Kashi na 01**

*بسم اله الرحمن الرحيم*

إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد

Assalamu Alaikum InshaAllah zan fara rubutu dan gane da Akidar Ahlussunnah wal'jama'ah Inda InshaAllah zan Kawo su kuma da dalilan su daga Al'kitabu Was-Sunnah A bisa Fahimatar Magabata na Kwarai!,

A wannan rubutu InshaAllah zan bi salo kamar Haka:-

*Ba Tsawaita rubutu,
*Kuma ba lallai na tafi a jere Kullum ba,
*Zan Taqaitu ga Kur'an da Hadisi Kamar yanda na gaya a baya bisa Fahimatar magabata,
*InshaAllah zan kokarin kawo maraji'I na abnd na kawo,

Kafin na Kutsa zan danyi Shimfida kadan Game da Akidar mu:-

Akida ta Ahlussunnah Wal'jama'ah Itace Addini Na Gaskiya Kuma Itace Akidar da Ta wajaba dukkan musulmi ya Kudurce domin Itace Hanyar da Annabi (s.a.w) da Sahabban shi suka bi, Yazo a Hadisi Annabi (s.a.w) yace:

"وستفترق هذه الأمة علي ثلاث وسبعين فرقة، كلها في النر إﻻ واحدة، قالو من هى يا رسول الله؟ قال : "من كان علي مثل ما أنا عليه وأصحابي"

Ma'ana: Annabi (s.a.w) yace:

"Da sannu wannan Al'umma zata rarraba izuwa kashi 73 Dukkan su suna wuta sai dai guda 1 (Sai Sahabbai) Suka ce: wacce ce Ita ya Ma'aikin Allah??
Sai Annabi (s.a.w) yace:
"Wadan da suka kasance akan abinda nake da sahabbai na"

[Tirmiziy 2641, Al'bani ya Inganta shi a صحيح الجامع 5343 ],

Idan muka kalli wannan Hadisi zamu ga Annabi (s.a.w) ya Siffanta wancan kashi da masu bin sa da kuma sahabban sa ma'ana Aikin su ya zama na aikin Annabi (s.a.w) ne da sahabban sa ba sabanin Hakan ba! Don Haka ashe riqo da Sunnar Annabi (s.a.w) wajibi ne ga duk mai son ya tsira a ranar Al'kiya ma,

Yazo a wani Hadisin Annabi (s.a.w) yace:

"عليكم بسنتي وسنة الخلفاء الرا شدين المهديين ، عضوا عليها با لنواجذ،"
Ma'ana:
"Na hore ku Da (yin riko) Da sunnata da Sunnar Khalifofi Shiryayyu, Kuyi riko Da Ita da Fikoki"

[Abu Dawud 4607, Tirmiziy 2676, Ibn Majah 42.]

Imamu Malik (R.H) yace:

"لن يصلح أخر هذه الأمة إﻻ بما صلح به أولها"
Ma'ana:
"(Mutanen) Karshe na wannan Al'ummah ba za su taba rabauta ba se da Abinda na Farkon ta suka Rabauta dashi"

Su waye na farkon??
Hanyar Su wa kenan??

Wannan ya kara Fassara Hadisin can na sama Don haka mu muka ce Sunnah Sak!!!!!

Kuma Ahlussunnah wadanda suka bi wannan Hanya Sune wadanda Allah Yake Taimaka A nan duniya. Kuma Itace Allah yake tseratar Da Ita a ranar Al'iyama,

Zamu tsaya anan se a rubutu na gaba,

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah),
27/04/2015,


**AKIDOJIN AHLUSSUNNAH Kashi na 02**

إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد

Cigaba..

Assalamu Alaikum. Yau zan dora daga Inda na tsaya a baya, yana da kyau ka karanta rubutun da ya gabata In baka karanta ba domin Fahimtar Inda muka dosa, Domin Karantawa shiga wannan rubutun na kasa:

http://www.basheerjournalistsharfadi.xtgem.com/akidojin%20ahlussunnah

In ba'a manta ba a rubtuna da ya gaba ta na tsaya ne akan:

Kuma Ahlussunnah wadanda suka bi waccan Hanya Sune wadanda Allah Yake Taimaka A nan duniya. Kuma Itace Allah yake tseratar Da Ita a ranar Al'iyama,

Yazo a wani Hadisi Ananbi (s.a.w) ya fada cewa: Babu wata Tawaga da ga cikin Al'umar sa da zata hadu a bisa gaskiya (Gaskiya Itace Bin wannan Hanyar da Annabi (s.a.w) ya siffanta a hadisin da muka kawo a baya) Sai Allah ya taimake ta, kamar yadda Muslim ya rawaito a 1920, Abi Dawu da Tirmiziy da Ibn majah Da Ahmad duk sun rawaito shi,

A cikin Al'kur'ani mai Girma Allah (s.w.a) yace:

"فأيدنا الذين ءامنو علي عدوهم فأصبحوا ظهرين"
Ma'ana:
"Sai muka Karfafi wadanda sukayi Imani akan Makiyan su, saboda Haka suka wayi gari suna masu rinjaye (Cin nasara)"

[Suratu الصف aya ta 14],

A wani gun Allah (s.w.a) yace:

"وإن جندنا لهم الغلبون"
Ma'ana:
"Kuma Hakika Rundunar mu sune Marabauta"

[Surats الصافات aya ta 173],

Wannan yana nuna mana Ahlussunnah ba'a rinjayar su da Hujja ko da Makami ko da wani Abu shi yasa Allah yake taimakon Ahlussunnah a dukkan Al'amuran su, Ga Kwarjinin da suke dashi a Idon Jama'a yanzu ko a cikin Abokanan ka In suka Fahimci kai mai Gaskiya ne mai Amana se kaji sunce da kai:-

"KAI se kace Dan IZALA??"

Kuma akidar Ahlussunnah da yace babu wani Kumbiya babu kwatance-kwatance Babu Bin Secular ba haushe yace ba'a yiwa gaskiya ado!! Allah (s.w.a) yace:

"فما ذا بعد الحق إﻻ الضلل"؟
Ma'ana:
"To menene A. Bayan Gaskiya face Bata?"

[Suratu ينوس aya ta 32],

Ahlussunnah Basu sakin Maganar Annabi (s.a.w) su kama ta wani ko wanene,

Zamu tsaya anan se a rubutu na gaba,

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah),
28/04/2015,


**AKIDOJIN AHLUSSUNNAH Kashi na 03**

إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد

Cigaba..

Assalamu Alaikum. Yau zan dora daga Inda na tsaya a baya, yana da kyau ka karanta rubutun da ya gabata In baka karanta ba domin Fahimtar Inda muka dosa, Domin Karantawa shiga wannan rubutun na kasa:

http://www.basheerjournalistsharfadi.xtgem.com/akidojin%20ahlussunnah

Su Ahlussunnah Basu da wani Suna Ko Lakabi da ake kiran su da shi Idan ba Sunnah ba, Se dai Ko Abinda ke nuni Izuwa ga Sunnar,

An tambayi Imamu Malik (R.H) akan : Suwaye Ahlussunnah ?? Sai yace:

"أهل السنة الذين ليس لهم لقب يعرفون به، ﻻ جهمي وﻻ قدري وﻻ رافضي"
Ma'ana:
"Ahlussunnah sune wadanda Basu da wani Lakabi da aka san su dashi, Ba Jahmiya Ko Kadariyya Ko rafidiyya"

[Duba كتب الإنتفاء na إبن عبد البر shafi na 35],

عبد الرحمن بن مهدي. Yace An Tambayi Imamu Malik game da Sunnah sai Yace.
"هي ماﻻ اسم له غيره السنة ، وتلي: "وأن هذا صرطي مستقيما فاتبعوه وﻻ تتبعوا السبل فتفرق بكم عن سبيله"
Ma'ana:
Imamu Malik yace: Ita Bata da wani Suna Face Sunnah' Sannan se ya karanto Fadin Allah (s.w.a) cewa:

"Kuma Hakika wannan ne Hanya ta madai-dai ci Sai Ku bi shi (hanyar ta sa), Kuma Kada Kubi wasu hanyo sai su rarrabu daku Ga barin Hanya ta"
[Sutul An'am aya ta 153],

[إمام الشاطبي ya fada a cikin الأعتصام 1/79],

Ibnul Qayyum Yake fada a cikin [ مدارج السالكين 3 /179] cewa an tambayi wani daga cikin A imma game da sunnah sai yace:

"ماﻻ إسم له سوي السنة"
Ma'ana:
"Basu da wani Suna Face sunnah"

Allahu Akbar shi yasa ba'a kiran mu da yan darikar wane... Se dai ajingina mu ga sunnar Annabi (s.a.w) Duk abinda za'a Kira mu dashi zaka ga yana komawa ne Izuwa ga Sunna, To Indai haka ne an raba kenan ku kun dauki naku muma mun dauki namu Shi ya sa idan kace dani:

AHLUSSUNNAH: Daman ni mabiyin Sunnar Annabi ne don haka kowa yana jingina kanshi da shehin sa don ya nuna wanda yake bi ni kuwa se ka jingina ni ga Lamba daya daman kuma ni shi nake bi shine nawa ganin,

In Ka Kirani da:

DAN IZALA: Se nai godewa Allah ka jingina ni ga Kungiyar dake Kauda Bidi'a Tana Tsaida Sunnah, Kungiyar dake Yada Addinin Allah Kaf Africa ynz ma duk duniya Izala ta ratsa, kuma daman ni Dan Izalar ne, Don Haka sai Hamdala,

In ka kirani:

DAN SALAFIYYA: Nan ma dai Kaya ya tsinke a gindin kaba ka siffantani da mai bin Tafakin magabata wanda mun kawo bayani a baya, Kuma dama ai tafarkin su shine abin bi,

In ka kirani:

BAWAHABIYE: Al'wahab Sunan Allah ne Kuma Ni bawan sane!

Allahu Akbar! Sunnah Hantsi Leka Gidan Kowa!!

Zan Tsaya Anan kuma nan ne karshen Yar shimfidar tawa kai tsaye kuma zan kutsa, se a rubutu na gaba,

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah),
29/04/2015,


*Koma Saman Shafi*

→Labarai

SUN JIMA SUNA BAYYANAWA A AIKACE! -Inji Imamu Ahlussunnah Sheik Abdulwahab Abdallah (H), (Basheer Journalost Sharfadi)

SUN JIMA SUNA BAYYANAWA A AIKACE!
-Inji Imamu Ahlussunnah Sheik Abdulwahab Abdallah (H),

-Shehin Malamin ya bayyana haka ne a daren yau Yayin walimar saukar Al'kur'ani mai Girma na Wasu Dattawa da kuma matasa da aka gudanar a Ungwuar Sudawa dake Kwaryar Birnin kano,
Sheik Abdulwahab yace:-

-''Suna kokarin Juya Suratul Kahfi su nuna wai Khadiru yafi Annabi Musa don su fake da akidar su,
-Don su nuna akwai wanda yafi Annabi, Kai Hatta Salati sun saki wanda Annabi (s.a.w) yazo dashi sun kama wanda wani ya kawo a cikin Mafarki,

-Irin su zaka ga an kira sunan wane Shehi sun Fadi suna Birgima wai Jazaba sbd tsananin soyayya Amman an kira sunan Annabi (s.a.w) ko Slaati basa Yi masa, Wallahi wadannan ba masoya manzo bane Karya suke!!

-Annabi (s.a.w) yace:

-''Imanin dayan ku baya cika har sai na kasance mafi soyuwa agare shi daga Yaya yan sa da Iyayen sa da mutane baki daya''

-Ya Dan uwa kada ka zama yan 'Wajad na Abaa ana''

-Kuma Wallahi Duk wanda ya taba Annabi Arnene ko wanene! Ko dan wanene!! Annabi (s.a.w) Ne Allah yace dashi:

-''WAMA ARSAL NAKA ILLA RAHMATAN LIL ALAMEEN''

-Ya yan uwa lokaci yayi a tashi ayi karatu Wadannan dake da'awar Suna Son Annabi wallahi Karya ne, Irin son kuraishawa ne da Gumakan su In an tambaye su suce ''Ai suna kamun Kafa da su ne zuwa ga Allah'' Amman kuma In an taba Gumakan nasu se su Zagi #Allah''

-Ga Shinan Mal. Mai Ishiriniyya ya kawa cewa''Busharar zuwan Annabi (s.a.w) tazo acikin Injila zabura Attaura,

-Akan wani waliyin ka da Injila zabura Hatta Kawa'idi be kawo shi ba, Wai Wali Ibrahim Inyass

-Waye san shi??
-Waye shi a Senegal Din??
-Kasar waje ya mutu,

-Wannan Mutumin yana magana yana nuna Jin Haushin Annabi (s.a.w) Me Annabi yayai maka??

-Wasu na cewa wai dan Allah mal. Kar ai mgn, wannan ba Nifaka bane a taba Ananbi sanan ace muyi shiru!

-Ana cewa muna kafurta Yan Darika Mu wallahi bama kafurta Su Amman duk wanda ya yarda Waliyin sa yafi Annabi Kafirine,

-Kuma wannan Shekarar Idan Allah ya bamu ruwa ganin damar sace wallahi,

-Yan Shehunnan nan a tskanin su an zagi wani suna ta wakoki amman an zagi Annabi Munafukai kunjisu shiru,

-Ina masu waka da tsalle suna cewa suna son Annabi?? Gashi an taba Annabi Munafukai kuna INa??

-Na tabbata da wani Shehi a ka taba Tuni an Kone garin,

A cewar Shin Malamin,

Muna Addu'ar Allah ka Tsinewa wadannan mutane da duk mai goyon bayan su,

Daga cikin mahalarta taron sun hada da:-

-Sheik Salis Ahmad Zage (Shugaban Jibwis Kano Municipal),
-Sheik Nura Umar Kofar Mata (Shugaban Majalisar Malamai na Jibwis Kano Municipal),
-Sheik Abdullah Ibrahim Daneji (Shugaban Madrisatu Tahfizul Kur'an Daneji), D.s

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah),
21/05/2015,

Back to posts
Comments:
[2015-10-11 14:17:57] Ibrahim Abdullahi :

Allah ya tsine musu matsiyata ku saki inyass ku kama Annabi (S.AW)

[2015-12-20 06:23:29] Mamanshakira :

Tnx

[2016-03-16 13:18:43] Usman yahaya :

Duk wawaye ne ku mara sa tunani kuna bakin ciki da baiwar da allah yaba inyass

[2016-03-31 08:21:46] Mubinat salis :

Allah ya shiryar damu hanya madaidaiciya

[2016-12-12 13:21:44] umar saleh rano :

Allah ya tabbatar damu akan sunnar Annabi (s a w)


UNDER MAINTENANCE

Share|

Kaima shiga a tattauna da kai
* No boards.

Online: Guests: 1


→Ra'ayin jama'a game damu

 IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:


Email: bjournalist55@hotmail.com

Phone No: 09035830253

Facebook: Basheer Journalist Sharfadi

Address: Ittihad Computer Centre,  No 92 Daneji Kano


MAI TALLA SHI KE DA RIBA


*Bayanan ka*
Browser din da ka hawo Mozilla

Kasar da kake United States

Adadin Maziyarta 297708

Adadin Wadanda Sukayi Comment 65691

A Wadanda Suka Shiga Tattaunawar Mu 54


Follow @bjournalist55
→Yi Adding Dina Ta Facebook
→Yi Like Na Dakarun Sunnah Page
→Yi Like Dina Ta Facebook

*Shafuka Masu Alaka Da Mu*

→Basheer Sharfadi wordpress
Basheer Sharfadi Blog Spot
UP
→Home

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah)
ISLAMIC DATE
  • phpimg2.php?it&ic=yellow



  • Click to Sms
    Click to Call


    Basheer journalist sharfadi3
    Coollogo com-1281358