Old school Swatch Watches
Google69490f6862051cb8
google-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlBasheer journalist sharfadi14

Basheer journalist sharfadi14.jpg6
Basheer journalist sharfadi 11 1
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka 1

☀ Zabi inda kake son shiga ☀
Menunks
→Home
→Akidojin Ahlussunnah
→Addinin musulunci (35)
→40 Hadith (50)
→Fadakarwa (120)
→Neman labarai (20)
→Shi'a Kafirci (50)
→Hadith (55)
→Khudubobi (24)
→Tarihin magabata (60)
→Raddi / Maida martani (99)
→Face book post (30)
→Monthly Archives (60)
→Tambaya da Amsa (20)
→Sahabban Annabi {s.aw} (50)
→Taskar maluman sunnah (25)
→Akidar Y'an Shi'a Dangane da Al'kur'ani
→Fassarar Usulussunnah (20)
→Sheik Ja'afar {Rahimahullah} (65)
→Sheik Abubakar Gumi {Rahimahullah} (30)
→Sheik Dr. Muhammad Sani R/Lemo
→Salafiyyah Network Nigeria (100)
→Adam Sani Abu-Umayrah (99)
→Salaf Ustaz (79)
→Malama Ummi Ahmad Katsina
→Malama Amina Saleh Mande
→Labarai (40)
→Nishadantarwa (10)
→Siyasar Nigeria (9)
→Vidio (33)
→Audio (66)
→Hotuna (120)
→Internet Cheat (90)
→Site Achieve
→Application (10)
→Games (8)
→About me (01)

Wannan shafin mallakarCoollogo com-1281358 3
Ne




SHAFI DON KARUWAR MUSULMI
**AKIDOJIN AHLUSSUNNAH Kashi na 01**

*بسم اله الرحمن الرحيم*

إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد

Assalamu Alaikum InshaAllah zan fara rubutu dan gane da Akidar Ahlussunnah wal'jama'ah Inda InshaAllah zan Kawo su kuma da dalilan su daga Al'kitabu Was-Sunnah A bisa Fahimatar Magabata na Kwarai!,

A wannan rubutu InshaAllah zan bi salo kamar Haka:-

*Ba Tsawaita rubutu,
*Kuma ba lallai na tafi a jere Kullum ba,
*Zan Taqaitu ga Kur'an da Hadisi Kamar yanda na gaya a baya bisa Fahimatar magabata,
*InshaAllah zan kokarin kawo maraji'I na abnd na kawo,

Kafin na Kutsa zan danyi Shimfida kadan Game da Akidar mu:-

Akida ta Ahlussunnah Wal'jama'ah Itace Addini Na Gaskiya Kuma Itace Akidar da Ta wajaba dukkan musulmi ya Kudurce domin Itace Hanyar da Annabi (s.a.w) da Sahabban shi suka bi, Yazo a Hadisi Annabi (s.a.w) yace:

"وستفترق هذه الأمة علي ثلاث وسبعين فرقة، كلها في النر إﻻ واحدة، قالو من هى يا رسول الله؟ قال : "من كان علي مثل ما أنا عليه وأصحابي"

Ma'ana: Annabi (s.a.w) yace:

"Da sannu wannan Al'umma zata rarraba izuwa kashi 73 Dukkan su suna wuta sai dai guda 1 (Sai Sahabbai) Suka ce: wacce ce Ita ya Ma'aikin Allah??
Sai Annabi (s.a.w) yace:
"Wadan da suka kasance akan abinda nake da sahabbai na"

[Tirmiziy 2641, Al'bani ya Inganta shi a صحيح الجامع 5343 ],

Idan muka kalli wannan Hadisi zamu ga Annabi (s.a.w) ya Siffanta wancan kashi da masu bin sa da kuma sahabban sa ma'ana Aikin su ya zama na aikin Annabi (s.a.w) ne da sahabban sa ba sabanin Hakan ba! Don Haka ashe riqo da Sunnar Annabi (s.a.w) wajibi ne ga duk mai son ya tsira a ranar Al'kiya ma,

Yazo a wani Hadisin Annabi (s.a.w) yace:

"عليكم بسنتي وسنة الخلفاء الرا شدين المهديين ، عضوا عليها با لنواجذ،"
Ma'ana:
"Na hore ku Da (yin riko) Da sunnata da Sunnar Khalifofi Shiryayyu, Kuyi riko Da Ita da Fikoki"

[Abu Dawud 4607, Tirmiziy 2676, Ibn Majah 42.]

Imamu Malik (R.H) yace:

"لن يصلح أخر هذه الأمة إﻻ بما صلح به أولها"
Ma'ana:
"(Mutanen) Karshe na wannan Al'ummah ba za su taba rabauta ba se da Abinda na Farkon ta suka Rabauta dashi"

Su waye na farkon??
Hanyar Su wa kenan??

Wannan ya kara Fassara Hadisin can na sama Don haka mu muka ce Sunnah Sak!!!!!

Kuma Ahlussunnah wadanda suka bi wannan Hanya Sune wadanda Allah Yake Taimaka A nan duniya. Kuma Itace Allah yake tseratar Da Ita a ranar Al'iyama,

Zamu tsaya anan se a rubutu na gaba,

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah),
27/04/2015,


**AKIDOJIN AHLUSSUNNAH Kashi na 02**

إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد

Cigaba..

Assalamu Alaikum. Yau zan dora daga Inda na tsaya a baya, yana da kyau ka karanta rubutun da ya gabata In baka karanta ba domin Fahimtar Inda muka dosa, Domin Karantawa shiga wannan rubutun na kasa:

http://www.basheerjournalistsharfadi.xtgem.com/akidojin%20ahlussunnah

In ba'a manta ba a rubtuna da ya gaba ta na tsaya ne akan:

Kuma Ahlussunnah wadanda suka bi waccan Hanya Sune wadanda Allah Yake Taimaka A nan duniya. Kuma Itace Allah yake tseratar Da Ita a ranar Al'iyama,

Yazo a wani Hadisi Ananbi (s.a.w) ya fada cewa: Babu wata Tawaga da ga cikin Al'umar sa da zata hadu a bisa gaskiya (Gaskiya Itace Bin wannan Hanyar da Annabi (s.a.w) ya siffanta a hadisin da muka kawo a baya) Sai Allah ya taimake ta, kamar yadda Muslim ya rawaito a 1920, Abi Dawu da Tirmiziy da Ibn majah Da Ahmad duk sun rawaito shi,

A cikin Al'kur'ani mai Girma Allah (s.w.a) yace:

"فأيدنا الذين ءامنو علي عدوهم فأصبحوا ظهرين"
Ma'ana:
"Sai muka Karfafi wadanda sukayi Imani akan Makiyan su, saboda Haka suka wayi gari suna masu rinjaye (Cin nasara)"

[Suratu الصف aya ta 14],

A wani gun Allah (s.w.a) yace:

"وإن جندنا لهم الغلبون"
Ma'ana:
"Kuma Hakika Rundunar mu sune Marabauta"

[Surats الصافات aya ta 173],

Wannan yana nuna mana Ahlussunnah ba'a rinjayar su da Hujja ko da Makami ko da wani Abu shi yasa Allah yake taimakon Ahlussunnah a dukkan Al'amuran su, Ga Kwarjinin da suke dashi a Idon Jama'a yanzu ko a cikin Abokanan ka In suka Fahimci kai mai Gaskiya ne mai Amana se kaji sunce da kai:-

"KAI se kace Dan IZALA??"

Kuma akidar Ahlussunnah da yace babu wani Kumbiya babu kwatance-kwatance Babu Bin Secular ba haushe yace ba'a yiwa gaskiya ado!! Allah (s.w.a) yace:

"فما ذا بعد الحق إﻻ الضلل"؟
Ma'ana:
"To menene A. Bayan Gaskiya face Bata?"

[Suratu ينوس aya ta 32],

Ahlussunnah Basu sakin Maganar Annabi (s.a.w) su kama ta wani ko wanene,

Zamu tsaya anan se a rubutu na gaba,

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah),
28/04/2015,


**AKIDOJIN AHLUSSUNNAH Kashi na 03**

إن الحمد لله نحمده ونستعينه ونستغفره ونعوذ بالله من شرور أنفسنا وسيات أعمالنا، من يهده الله فلا مضل له، ومن يضلل فلا هادي له وأشهد أن ﻻ إله إﻻ الله وحده ﻻ شريك له، وأشهد أن محمدا عبده ورسوله، أما بعد

Cigaba..

Assalamu Alaikum. Yau zan dora daga Inda na tsaya a baya, yana da kyau ka karanta rubutun da ya gabata In baka karanta ba domin Fahimtar Inda muka dosa, Domin Karantawa shiga wannan rubutun na kasa:

http://www.basheerjournalistsharfadi.xtgem.com/akidojin%20ahlussunnah

Su Ahlussunnah Basu da wani Suna Ko Lakabi da ake kiran su da shi Idan ba Sunnah ba, Se dai Ko Abinda ke nuni Izuwa ga Sunnar,

An tambayi Imamu Malik (R.H) akan : Suwaye Ahlussunnah ?? Sai yace:

"أهل السنة الذين ليس لهم لقب يعرفون به، ﻻ جهمي وﻻ قدري وﻻ رافضي"
Ma'ana:
"Ahlussunnah sune wadanda Basu da wani Lakabi da aka san su dashi, Ba Jahmiya Ko Kadariyya Ko rafidiyya"

[Duba كتب الإنتفاء na إبن عبد البر shafi na 35],

عبد الرحمن بن مهدي. Yace An Tambayi Imamu Malik game da Sunnah sai Yace.
"هي ماﻻ اسم له غيره السنة ، وتلي: "وأن هذا صرطي مستقيما فاتبعوه وﻻ تتبعوا السبل فتفرق بكم عن سبيله"
Ma'ana:
Imamu Malik yace: Ita Bata da wani Suna Face Sunnah' Sannan se ya karanto Fadin Allah (s.w.a) cewa:

"Kuma Hakika wannan ne Hanya ta madai-dai ci Sai Ku bi shi (hanyar ta sa), Kuma Kada Kubi wasu hanyo sai su rarrabu daku Ga barin Hanya ta"
[Sutul An'am aya ta 153],

[إمام الشاطبي ya fada a cikin الأعتصام 1/79],

Ibnul Qayyum Yake fada a cikin [ مدارج السالكين 3 /179] cewa an tambayi wani daga cikin A imma game da sunnah sai yace:

"ماﻻ إسم له سوي السنة"
Ma'ana:
"Basu da wani Suna Face sunnah"

Allahu Akbar shi yasa ba'a kiran mu da yan darikar wane... Se dai ajingina mu ga sunnar Annabi (s.a.w) Duk abinda za'a Kira mu dashi zaka ga yana komawa ne Izuwa ga Sunna, To Indai haka ne an raba kenan ku kun dauki naku muma mun dauki namu Shi ya sa idan kace dani:

AHLUSSUNNAH: Daman ni mabiyin Sunnar Annabi ne don haka kowa yana jingina kanshi da shehin sa don ya nuna wanda yake bi ni kuwa se ka jingina ni ga Lamba daya daman kuma ni shi nake bi shine nawa ganin,

In Ka Kirani da:

DAN IZALA: Se nai godewa Allah ka jingina ni ga Kungiyar dake Kauda Bidi'a Tana Tsaida Sunnah, Kungiyar dake Yada Addinin Allah Kaf Africa ynz ma duk duniya Izala ta ratsa, kuma daman ni Dan Izalar ne, Don Haka sai Hamdala,

In ka kirani:

DAN SALAFIYYA: Nan ma dai Kaya ya tsinke a gindin kaba ka siffantani da mai bin Tafakin magabata wanda mun kawo bayani a baya, Kuma dama ai tafarkin su shine abin bi,

In ka kirani:

BAWAHABIYE: Al'wahab Sunan Allah ne Kuma Ni bawan sane!

Allahu Akbar! Sunnah Hantsi Leka Gidan Kowa!!

Zan Tsaya Anan kuma nan ne karshen Yar shimfidar tawa kai tsaye kuma zan kutsa, se a rubutu na gaba,

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah),
29/04/2015,


*Koma Saman Shafi*

→Labarai

KIFI NA GANIN KA MAI JARKOMA Kashi ta 11 (Basheer Journalist Sharfadi)

KIFI NA GANIN KA MAI JARKOMA Kashi ta 11 (Basheer Journalist Sharfadi)

-A jiya Al-hamis Kamar yadda sanarwa ta gabata an gabatar da wannan gagarumar Lakca a karo na farko Bayan dawowa daga Hutun Azumin watan Ramadan.

-Lakcar wadda aka gabatar a Masallacin Jumu'a na Triumph dake Kano ta gudana ne karkashin Jagorancin Mataimaki na (2) Ga shugaban Kwamitin Jibwis Social Media na Kasa Kuma Turakin Sa'in Fika. Alaramma Anas Assalafiy Fagge.

-Inda Matashin Malami Sheik Kabir Basheer Abdul-hamid (Hayaki Fidda na Kogo) ya Gabatar. Shehin Malamin Ya Haska Idon Mal. Sarki ciki da waje Inda aka danna shi ya fada da Bakin sa sannan aka bashi amsa.

-Acikin Lakcar jiyan dai an cigaba da Tono Tabagrgazozin Mal. Audu wazirin Shi'a a gefe guda kuma Lakcar ta Jiya ta dan dauki wani Sabon Salo na Sababbin Jini.

-Bayan da Mal. Kabiru ya dakata da sauke ruwan dalilai sai aka gayyato daya daga cikin Takubban Sunnah Akan Mal. Sarki. Ustaz Abdurrazaq Uba Musa Inda Shima ya Kara Haska Fitilarsa har zuwa Filin Mushe. daga Bisani Kuma Mal. Baba Uba K/wambai Shima ya kara sai tata Kwanar Fadar Sarkin kogon.

-A karshe dai Secretary Kwamitin saminer na Kungiyar Izala ta Kasa Sheik Abubakar Abdussalam Baban Gwale ya karasa kutsawa kai tsaye zuwa ga fadar Mal. Audu Inda yayi Ta'aliki na karshe.

•A jiyan dai an bada bayanai masu fa'ida gamida War-ware shubuhohi Irin na Dan Gidan Mai waka.

•Ku cgb da kasancewa da mu Ko wane Lokaci daga yanzu domin samun Audio din Lakcar.

Basheer Journalist Sharfadi Abu Hafsah.
07/08/2015.

Back to posts
Comments:
[2016-04-18 12:44:25] nana khadeeja :

Muna godiya matuqa da irin wannan qoqari dakukeyi wajen yada da awa ta magabatammu Allah yagartamusu Ameen mukuma Allah yabamu cikawa da imani

[2016-04-18 12:50:27] khadeeja Abubakar :

NAS ALULLAHA LANA WALAKUMUL AFIYA WASSALAAMAH

[2016-06-03 07:11:46] alhousseini :

allah ka karama malammamu illimi sa taka

[2016-12-28 10:20:14] SHAMSIYA ABUBAKAR :

ALLAH YA KARAWA MALAMANMU TSAWO KWANA MAI ALBARKA

[2017-03-12 07:36:49] bashir usman :

Assalamu Alaikum yan uwa musulmai bayan sallama irinta addinin musulunchi don Allah inna son number mal Aminu daurawa


UNDER MAINTENANCE

Share|

Kaima shiga a tattauna da kai
* No boards.

Online: Guests: 2


→Ra'ayin jama'a game damu

 IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:


Email: bjournalist55@hotmail.com

Phone No: 09035830253

Facebook: Basheer Journalist Sharfadi

Address: Ittihad Computer Centre,  No 92 Daneji Kano


MAI TALLA SHI KE DA RIBA


*Bayanan ka*
Browser din da ka hawo Mozilla

Kasar da kake United States

Adadin Maziyarta 293018

Adadin Wadanda Sukayi Comment 65691

A Wadanda Suka Shiga Tattaunawar Mu 54


Follow @bjournalist55
→Yi Adding Dina Ta Facebook
→Yi Like Na Dakarun Sunnah Page
→Yi Like Dina Ta Facebook

*Shafuka Masu Alaka Da Mu*

→Basheer Sharfadi wordpress
Basheer Sharfadi Blog Spot
UP
→Home

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah)
ISLAMIC DATE
  • phpimg2.php?it&ic=yellow



  • Click to Sms
    Click to Call


    Basheer journalist sharfadi3
    Coollogo com-1281358